Ademola Lookman ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na Africa

Lookman lokacin da ya karbi kyautar gwarzon dan wasa

Dan wasan tawagar Nijeriya Super Eagles, Ademola Lookman ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na nahiyae Africa.

Lukman ya doke zaratan yan wasa irin Ronwen Williams na Africa ta kudu da Simon Adingra na Cote d’Ivoire sai Achraf Hakimi na Morocco da Serhou Guirassy na kasar Guinea wajen lashe kyautar.

An gudanar da bikin karrama gwarazan 'yan wasan na Africa ne a a birnin Marrakech na kasar Morocco.

Lashe kyautar ta sa na nuni da cewa har yanzu kambun yana Nijeriya, domin kuwa dan wasa Victor Osimhen ne na tawagar Super Eagles ya lashe kyautar a shekarar 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp