A shirye nake na fuskanci sabon kalubale - Rashford

Marcus Rashford 

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya ce a shirye ya ke ya fuskanci sabon kalubale.

Rashford ya bayyana hakan ne lokacin da aka tambaye shi game da makomarsa a kungiyar ta United. 

Mai shekaru 27, an cire shi daga cikin 'yan wasa a wasan da United ta doke Manchester City da ci 2 da 1. 

Sabon mai horas da yan wasan kungiyar Ruben Amorim yace ba bu yanayin ladabtarwa bayan hukuncin da ya yanke, sai dai ya yi fatan ganin sauyi daga dan wasan na Ingila.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp