Bayanai na nuna cewa za a gudanar da jana'izar babban hafsan sojin kasa na Nijeriya margayi Laftanar Janar Taoreed Lagbaja tare da binne shi a wannan jumu'a.
Dan uwan margayin, Moshood Lagbaja ne ya bayyana hakan a birnin Osogbo na Jihar Osun, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
A cewarsa, har yanzu rundunar soji bata hannunta gawar margayi Taoreed Lagbaja ga iyalinsa ba, sai dai ya bada tabbacin cewa za a yi masa jana'iza tare da binne shi a birnin Abuja a wannan jumu'a.
Idan musulmi ne Allah ya gafarta masa.
ReplyDeleteIdan kafiri ne Allah kara masa nauyin kasa