Za mu shirya wa Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya zanga-zanga idan bai gyara lamurransa ba - Magoya bayan APC


Gamayyar kungiyoyin da ke goyon bayan jam'iyyar APC a Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta bukaci sakataren gwamnatin tarayya George Akume da ya hada kan jam’iyyar da shugabannin jam’iyyar a yankin Arewa ta tsakiya.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, bayan taron kungiyar a Abuja, ta kuma yi kira ga sakataren Gwamnatin tarayyar da ya tsaya a matsayin shugaban jam’iyyar a shiyyar Arewa ta tsakiya ta hanyar tabbatar da cewa al’ummar yankin Arewa ta tsakiya sun mori irin salon mulkin Shugaba Tinubu.

Kungiyar ta yi gargadin cewa za ta shirya zanga-zangar adawa da sakataren gwamnatin tarayya idan ya kasa daukar matakan gaggawa don gyara rashin daidaiton nade-naden nasa, da kuma magance kura-kurai a tsarin shugabancinsa.

A cewar kungiyar, Mr George Akume ya kamata ya dauki dukkan shiyyar Arewa ta Tsakiya a nade-naden mukamai da ofishin sa ya yi.

Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya bai ci gajiyar mukaman da George Akume ya nada ba.

Sanarwar ta tunasar da sakataren gwamnatin cewa ya ci albarkacin yankin Arewa ta tsakiya ne aka nada shi mukamin, amma ya buge da nada 'yan'uwansa 'yan kabilar Tiv kadai a mukaman da yake badawa a ofishinsa.

Saleh Zazzaga ya yi kira ga Sanata George Akume da ya gyara wannan abin da suka kira barna, ko kuma su shirya masa zanga-zanga don nuna fushinsu a kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp