Za mu sake gabatar da kudurin wa'adin shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnoni, inji dan majalisar da ya kawo kudurin, Ikenga Ugochinyere


Dan majalisar wakilan Nijeriya da ke jagorantar gabatar da kudurin kara wa'adin shugaban kasa da gwamnoni Ikenga Ugochinyere (PDP, Imo) ya ce za su sake gabatar da kudurin wanda majalisa ta ki amincewa da shi a zamanta na ranar Alhamis.

Wannan kudurin, ko baya ga neman kara wa'adin zuwa shekara shida, na son a gudanar da zabe a matakin kasa da jihohi a rana daya tare da yin tsarin karba-karba na shugabanci tsakanin yankin arewa da kudancin Nijeriya.

Sai dai bayan sake gabatar da kudurin karo na biyu, 'yan majalisar sun yi watsi da shi ba tare da bada damar tattaunawa a kai ba.

Duk da haka, dan majalisar Ugochinyere, a cikin wani bayani da ya fitar, ya sha alwashin sake gabatar da kudurin bayan yin tuntuba domin ganin cewa sun yi nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp