Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa jam’iyyar su ta PDP za ta yi duk mai yuwa wajen gyara Nijeriya dama jam’iyyar da a yanzu take ta fama da rikicin cikin gida.
Makinde ya fadi hakan ne a Abuja a wajen kaddamar da wani kwamitin gwamnoni da samar da tsarin dimokuradiyya.
Makinde ya ce “za mu gyara jam’iyyar mu ta PDP sannan PDP za ta gyara Nijeriya don ceto al’ummar kasar daga halin da suke ciki.