Za a dakatar da daliban da ke tsangwamar abokan karatunsu - Gwamnatin Nijeriya


Ma'aikatar ilimi ta tarayya ta yi gargadin cewa duk dalibin da aka samu da laifin cin zarafin da ya kai ga taba lafiyar abokan karatunsu, za a dakatar da shi daga kwalejojin tarayya har sai yadda hali yayi.

Wata takardar umurni da babban sakataren ma'aikatar, Nasir Gwarzo, ya sanyawa hannu ta ce ba za su zuba ido dalibai na raunata junansu ba a cikin makarantu.

Sanarwar ta ce ko a ranar 7 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta bada umurnin dakatar da wasu dalibai 13 na tsawon makonni 6 a jihar Enugu har sai an gudanar da bincike kan zargin da ake musu na tsangwamar abokan karatunsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp