Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce jami'an 'yan sandan Nijeriya sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce iyaka akan masu zanga-zangar #EndBadGovernance.
Zanga-zangar ta faru ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024, sanadiyar halin matsin rayuwa da 'yan ƙasar ke fuskanta.
Wani rahoto da kungiyar Amnesty ta fitar, ya ce mutum 24 aka kashe, yayinda aka kama sama da mutum 1,200 ciki har da ƙananan yara a lokacin zanga-zangar.
Kungiyar ta bukaci a yi bincike domin hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aikar.
Category
Labarai