Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da kama wasu karnuka uku da ake zargin sun hallaka wani mai gadi a unguwar Pinnock Estate da ke Ilasan a yankin Lekki na jihar.
‘Yan sandan sun kuma kame mamallakin karnukan mai suna Salisu Mustapha.
Jami'an na yan sanda sun kuma bayyana cewa karnukan suna samun kyakkyawar kulawa a wajen su domin kaucewa tauye hakkin dabbobi.
Nice
ReplyDelete