Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin karfen layin dogo ne tare da kwato mayan karafa guda 40 da suka sata a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Kaduna.
Hassan ya bayyana cewa wani mutum mai suna Yusuf Dogo, daga kungiyar ‘yan banga a Gnami a karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna ne ya zo ofishin ‘yan sanda inda ya kawo rahoton cewa ya ga wasu da ake zargin suna lalata hanyar jirgin kasa a Gnami.