Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa Cif Bode George ya ce 'yan Nijeriya na shirin juyawa gwamnatin Tinubu ta jam'iyyar APC baya a zaben shekara ta 2027 da ke tafe.
Bode George wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai don bikin cikarsa shekaru 79, ya yi fatar cewa PDP za ta nutsu don dinke duk wata baraka da ke ciki don ceto 'yan Nijeriya daga mulkin APC.
Ya bayyana rashin jin dadi akan yadda wasu marar kishi a jam'iyyar su ka hada kai da APC wajen yi wa PDP makarkashiya a zaben 2027, inda ya ce dole a taka musu burki.
George, ya nuna cewa PDP ce kawai za ta iya ceton 'yan Nijeriya daga halin da su ke ciki, amma dole sai sun hada kai za su cimma hakan.