'Yan majalisar wakilai sun yi watsi da kudirin wa'adin mulki na shekara 6 ga shugaban kasa da gwamnoni.
Majalisar wakilai ta Nijeriya sun yi watsi da kudirin wa'adin mulki na shekara 6 ga shugaban kasa da gwamnoni da aka sake gabatarwa domin zaman karatu na biyu.
Majalisar ta yi watsi da kudurin ne a zaman ta na ranar Alhamis.
Kudirin wanda dan majalisar Ikenga Imo Ugochinyere da wasu 'yan majalisa 33 su ka gabatar, na kuma neman a rika gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni da yan majalisa a rana daya.