Donald Trumph/Kamala Haris |
A yau ne 5 ga watan Nuwamba 'yan kasar Amurka za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar, inda za a kara tsakanin Kamala Harris da ke jam'iyyar Democrat da Donald Trump da ke jam'iyyar Republican.
Zaben, wanda kasashen duniya da dama ke sanya ido a kai, ya kuma hada da zaben 'yan majalisar dokoki kasar, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara dokoki a Amurka.
Wanda ya yi nasara a cikin su zai yi aiki na tsawon shekaru hudu, wanda zai fara daga Janairu 2025.