Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas |
'Yan bindigar dai sun halaka manomin mai suna Alhaji Mai Wanda Maibultu a gonar sa a karshen makon da ya gabata,wanda yana daya daga cikin manyan manoma a kauyen.
Daily Trust ta rawaito cewa sauran manoma shidan da aka yi garkuwa da su,suna kauyen Garbatau, da ke tsakanin tsaunuka biyu a yanki.
Wani mazaunin garin Maihula, Adamu Dauda, ya shaida wa Daily Trust cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi iyalan manoman da suka sace, inda suka nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.
Ya ce, ko a shekarar da ta gabata daruruwan masu garkuwa da mutane sun addabi yankin tare da yin garkuwa da manoma da dama, inda suka hana su girbin amfanin gonakinsu.