Gwamnan Kaduna Uba Sani |
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kona masara a gonaki shida a kauyen Kwaga da Unguwar Zako da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Mutanen garin, musamman ma masu gonakin da abin ya shafa, sun shiga cikin firgici, inda suka koka da asarar da harin ya janyo musu a gonaki.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi inda ‘yan bindigar suka far wa gonakin tare da kona duk masarar da aka girbe.
Wani daga ciki masu gonakin da abin ya shafa Kabiru Halilu Kwaga,ya shaida wa Daily Trust cewa ya girbe buhunan masara sama da 160 a shekarar da ta gabata kuma ya yi fatan samun girbi mai yawa a bana, sai dai kuma maharan sun kona dukkan amfanin gonar ta sa.
Surajo Kwaga,shima wanda ya girbe buhunan masara 40 a gonarsa a shekarar da ta gabata, ya kuma yi asarar amfanin gonarsa gaba daya bisa kona ganakin nasu da 'yan bindigar sukai.