Rahotanni daga jihar Niger na cewa masu garkuwa da mutane sun sace akalla fasinjoji 20 da suke a cikin motoci biyar yayin da suke kan hanyar Mariga zuwa Kontagora.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazabar Mariga, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema a ranar Juma’a a garin Minna babban birnin jihar.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da ‘yan bindiga suka tare hanyar Mariga zuwa Kontagora tsakanin Baban-Lamba da Beri.
Jihar Niger da daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya