'Yan bindiga sun halaka mutum biyar tare da kona shaguna a Zamfara

 





Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a kauyen Dayau na karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun yi ajalin mutam biyar tare da kona wasu gidaje da shaguna da rumbun ajiyar abinci da dama a kauyen. 


Wani mazaunin garin mai suna Shamsu, ya shaida wa jaridar Premium times cewa ‘yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i bakwai suna cin karen su ba babba ka.


Ya kara da cewa yan bindigar sun shigo garin ne ta hanyar Kungurki a kan babura, amma ‘yan banga da jami’an tsaron al’umma sun shafe sama da sa'a day sun na arangama kafin yan yan bindigar su gudu.


Mutumin ya ce bayan sun sake dawowa ne suka shammaci jami'an, inda wasu suka riƙa harbin mai uwa da wabi wasu kuma suka kona gidaje da shaguna.


Duk kokarin da Premium Times ta yi na jin ta bakin jami’in yada labarai na rundunar yan sandan jihar Zamfara hakan ya ci tura.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp