Yahaya Bello ya shiga hannun hukumar EFCC


Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya shiga hannun hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya bisa zargin badakalar kudade. 

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar jami'an hukumar na yi wa tsohon gwamnan tambayoyi.

Wasu rahotanni sun ce hukumar ce ta kama shi, inda wasu ke cewa Yahaya Bello ne ya kai kan sa ofishin hukumar tare da lauyoyinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp