Hukumar EFCC yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya dake Maitama, Abuja.
Yahay Bello, wanda ya rika wasar buya da hukumar tun a watan Afrilun 2024, na tsare a hannun hukumar tun jiya Talata.
An gurfanar da shi ne a gaban Mai Shari'a Maryanne Anenih, tare da wasu Umar Oricha da Abdulsalami Hudu bisa zarge-zarge 16 na almundahana da naira biliyan 110.
Category
Labarai