Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Birnin Gwari na jihar a lokacin da ya karbi kason farko na 'ysn ta'addar da suka tuba suka rungumi sulhu a jihar.
Kazalika, Gwamnan ya ma umurci da a Bude kasuwar shanu ta Birnin Gwari da aka rufe shekaru 10 da suka gabata saboda dalilai na tsaro.
Sanata Uba Sani ya ce jihar na zama da wasu hukumomin gwamnatin tarayya don tattaunawa da 'yan ta'adda da nufin su ajiye makamansu a dawo da zaman lafiya yadda ys dace.