Wasu mahara sun sace mutum hudu 'yan gida daya a jihar Kaduna

 


Al'ummar yankin Keke A dake rukunin gidajen Kaduna Millennium City sun shiga firgici, bayan sace wani yaro dan shekaru biyu tare da 'yan uwansa mata uku da wasu 'yan ta'adda suka yi.

An ruwaito cewa, matan wadanda aka sace 'yan shekaru 9, da 12, da kuma 15 ne, kuma daya daga cikinsu marainiya ce. kamar yadda mahaifin yaran Yunusa Sarkin Samarin Keke ya shaidawa jaridar Dailytrust.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Talata, lokacin da mahaifin yaran ya tafi asibiti domin duba mahaifiyar yaran wadda ke kwance a asibiti.

Duk kokarin jin ta bakin kakakin 'yan sandan jihar Kaduna ASP Mansur Hassan hakan ya ci tura, kuma bai mayar da sakon waya da aka tura masa ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp