Wasu mutane da har ya zuwa hada wannan rahoton, ba a san ko su wanene ba, sun yi wa wata budurwa mai suna Maryam Salisu Dangabas sanadin mutuwa a garin 'Yanduna na karamar hukumar Baure jihar Katsina.
Bayanan da DCL Hausa ta samu daga makusantan budurwar mai kimanin shekaru 17 na nuna cewa ana zargin miyagun kafin su yi wannan aika-aika sai da suka kawar mata da budurcinta.
DCL Hausa ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina inda kakakin rundunar Aliyu Abubakar Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rundunar 'yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Tuni aka yi jana'izar marigayiya Maryam Salisu kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin na 'Yanduna.