Wani abu mai hatsari ya tarwatse a birnin Jos


Wata fashewa mai karfi ta faru a birnin Jos na jihar Plateau da safiyar yau Talata, lamarin da ya jefa al'umma cikin fargaba. 

Shaidun gani da ido sun shida wa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na safe a kusa ga Kasuwar Terminus. 

Rahotanni sun ce mutane da dama sun jikkata sanadiyar fashewar, akwai fargabar cewa an rasa rayuka. 

Sai dai har yanzu rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai ba a hukumance.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp