WAEC, ta haramta wa wasu makarantu 13 a jihar Kogi yin jarrabawar, bisa zargin su da satar jarrabawa a shekarar 2023/2024

 

WAEC


Kwamishinan Ilimi na jihar, Wemi Jones ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da suka yi da wasu shugabanni da masu kula da WAEC.


Ya ce gwamnati ta sha alwashin hukunta shugabannin makarantu da malaman da suke kula da dalibai suka taimaka wajen lalata harkar jarrabawa a jihar.


Jones ya jaddada cewa aikata hakan babban laifine kuma gwamnati za ta hukunta duk wanda ta kama yana da hannu a ciki,daga yanzu za a gurfanar da duk wanda aka kama da aikata laifin satar jarabawa kuma a gurfanar da shi gaban kotu kamar yadda dokar ilimi ta jihar Kogi ta tanada.


Ya bayyana cewa za a kafa wani kwamiti wanda babban sakatare na ma’aikatar ilimi zai jagoranta domin bincikar mutanen da WAEC ta ke tuhumar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp