Tsadar magani ta sa an fara kaurace wa zuwa asibiti jinyar marasa lafiya a Nijeriya
- Likita
Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD) na asibitin kwararru da ke Jalingo a jihar Taraba, Alex Maiangwa, ya ce ba a samun marasa lafiya a asibitocin jihar
Ya bayyana kalubalen tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar ya sa masu marasa lafi ba su iya kawo su asibiti domin yin jinya
Inda ya ce yanayin da ake ciki ya tilasta wa mutane bullo sa wasu hanyoyi na jinya a gida Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD) na asibitin kwararru na jihar Taraba, Jalingo, Alex Maiangwa, ya ce asibitocin jihar suna samun karancin halartar masu zuwa.