Tinubu ya isa kasar Saudiyya domin halartar taro na kasashen Musulmi

 



Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da misalin karfe 10 na safe agogon kasar, inda mataimakin gwamnan birnin Riyadh, Yarima Mohammed Bin Abdulrahman Bin Abdulaziz ya tarbe shi.


Shugaba ya amsa gayyatar mahukuntan kasar ta Saudiyya domin halartar wani taro na kasashen Musulmai da za a yi a birnin Riyadh, shelkwatar kasar. 


Bayanai daga fadar shugaban Nijeriya sun ce shugaban ya samu rakiyar ministan yada labarai da Malam Nuhu Ribadu mai ba da shawara kan tsaro da shugaban hukumar leken asirin Nijeriya

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp