Tinubu ne matsalar PDP a Nijeriya - inji wani jigo a jam'iyyar, Segun Sowunmi


 Tinubu ne matsalar PDP a Nijeriya - inji wani jigo a jam'iyyar, Segun Sowunmi

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya dora alhakin rikicin da ke ciki gida dake faruwa a jam’iyyar bisa kan mukamin da shugaban Bola Tinubu ya baiwa Nyesom Wike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja.

Segun Sowunmi ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, lokacin da aka tambaye shi game da matsalar PDP.

Ya ce mutane na dora matsalar kan Wike ne kawai amma yana ganin Tinibu ne matsalar, domin bai tuntubi shugabannin jam'iyyar kafin bashi wannan matsayi ba.

Segun ya yi nuni da cewa ko a lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa gwamnatin hadin kan kasa sai ya  tuntubi jam’iyyun adawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp