Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayarda hankali wajen saka jari a bangaren noma da kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shugaban wanda ke jawabi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, ya kuma jaddada cewa akwai matsalar yunwa a kasar, sai dai gwamnatin sa na kokarin ganin abubuwa sun daidaita.
Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake sanya hannu ga wata yarjejeniyar saka hannun jarin dala biliyan 2.5 da kamfanin JBS S.A, daya daga cikin manyan kamfunnan da ke sarrafa nama a fadin duniya.
Ya ce wannan yarjejeniya za ta magance matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya da ta jima tana damun al'umma a wannan nahiya.