Sufeton 'yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin bincike kan cin zarafin yaran da aka kama yayin zanga-zangar#BadGovernance

Kayode Egbetokun


Babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin zarafin kananan yara da aka kama yayin zanga-zangar #BadGovernance


 Jaridar PUNCH  ta rawaito cewa a ranar Juma’a, an gurfanar da mutane 76 da ake zargi, galibinsu kananan yara da ba su samu isasshen abinci mai gina jiki ba,shida daga cikin yara kanana sun fadi a wajen shari'ar hakan yasa aka a fitar da su daga wurin shari’a domin samun agajin gaggawa.


Da yake mayar da martani game da lamarin a ranar Asabar, IG ya yi iƙirarin cewa suman da wasu yara ƙanana sukai a kotun an shirya shi ne don jawo hankulan mutane.


Bayan da al'umma suka nuna bacin ransu kan lamarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a janye tuhumar da ake yi wa kananan yaran.                    


A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Muyiwa Adejobi ya fitar a daren ranar Litinin, ya bayyana cewa IG ya bayar da umarnin gudanar da bincike yaran a lokacin da suke tsare.


 Adejobi ya kara da cewa, da samun rahoton binciken, IG ya sha alwashin magance duk wasu kura-kurai da aka gano.


 Ya ce babban sufeton ‘yan sandan , yayin da yake birnin Algiers na kasar Aljeriya don halartar taron kwamitin hadin gwiwar ‘yan sanda na kungiyar Tarayyar Afirka, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp