Hedikwatar tsaron Nijeriya ta sanar da nasarar kama wani kasurgumin dan ta'adda mai suna Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Habu Dogo a Sokoto da karin wasu kwamandojin kungiyar 'yan a ware ta IPOB a kudu maso Gabas.
Daraktan yada labaran hedikwatar tsaron Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce an yi nasarar kama Habu Dogo ne a kauyen Rumji na karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto.
A cewarsa, Habu Dogo na cikin jerin 'yan bindigar da jami'an tsaro ke nema ruwa jallo a Nijeriya da ma makwabciya jamhuriyar Nijar saboda yanayi n ayyukan ta'addancinsa.
Su kuwa kwamandojin kungiyar 'yan a waren ta IPOB da sojojin suka yi nasarar kamawa sun hada da Dr Nnamdi Chukwudoze da Chigozie Ezetoha da aka fi sani da Chapet da aka kama su a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Sauran su ne Mrs Ngozi Chukwuka da Mr Oyekachi Ohia da aka kama a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia da dai sauransu.