Sojojin Nijeriya sun fatattaki 'yan kungiyar Lakurawa a jihohin Kebbi da Sokoto

 





Rundunar sojojin Nijeriya ta ce ta tura dakarunta zuwa jihohin Sokoto da Kebbi inda su ka fatattaki 'yan kungiyar Lakurawa a wasu sansanonin su da ke yankin 


Hakan ya biyo bayan wani hari da kungiyar ta Lakurawa da ta kai wa al’ummar garin Mera da ke karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 17 


A cewar mai taimaka wa gwamnan jihar Kebbi a harkokin yada labarai,  Abdullahi Idris Zuru, sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kwato shanu da dama da suka kwacem


A kwanannan gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo daukin gaggawa domin kakkabe sabuwar kungiyar ta Lakurawa, da ke yin ta'adi a yankunan karkara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp