Sojoji |
Sojojin Nijeriya da 'yan sintirin Vigilante sun shafe kusan sa'o'i 9 suna artabu da rikakken dan bindigar nan, Bello Turji, a garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Majiyoyi da dama daga garin na Gatawa sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa an fara artabun da ‘yan bindiga da tun da misalin karfe 6 na safiyar Talatar nan.
Daya daga cikin majiyoyin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun yi yunkurin kutsawa cikin garin na Gatawa, amma sojoji da 'yan sintirin suka hana su.
Kazalika, majiyar ta ce ana zargin Bello Turji ne da kansa ya jagoranci 'yan bindigar zuwa yankin.
A cewar majiyar an fara musayar wutar da misalin karfe 6 na safe har zuwa uku saura kwata na yammacin Talatar nan.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu wata sanarwa a hukumance daga jihar ta Sokoto game da wannan musayar wuta.