Sojoji sun halaka ‘yan fashin daji 481, sun kuma kama wasu 741, tare da ceto mutane 492 a watan Oktoba

Sojojin Nijeriya


Akalla ‘yan fashin daji 481 ne aka halaka su, an kuma kama wasu 741, yayin da sojojin Nijeriya kuma suka kubutar da mutane 492 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Oktoba, kamar yadda hedkwatar tsaro ta bayyana a ranar Alhamis.


Daraktan yada labaran hedkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato makamai 480 da alburusai kala-kala 9,026.


Ya kuma ce makaman da aka kwato da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 263, bindigogi kirar gida guda 81, bindigogi samfurin waje 91,sai kuma karin wasu bindigogin guda 76, wanda adadin su yakai 5,683. 


Maj Janar Buba ya ci gaba da cewa ‘yan fashin dajin ba za su iya kwatanta karfin su da na soji ba, ya kuma umurce su da su ajiye makamansu su mika wuya ga sojoji ko kuma su kasance cikin shirin fuskantar fushin sojoji.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp