Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede ya isa jihar Sokoto ziyarar aiki ta farko a daidai lokacin da aka gano wata sabuwar kungiyar 'yan bindiga da ake kira da Lakurawa.
A yayin wannan ziyara ana sa ran zai gana da masu ruwa da tsaki da kuma ziyartar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi
Zai yi amfani da damar wajen yin jawabi ga dakarun Operation Fasan Yamma da ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.