Shugaban Nijeriya ya bukaci majalisar dokokin kasar ta amince da ciyo sabon bashin Naira Tiriliyan 1.7 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2024.

 



Shugaban Tinubu ya bukaci majalisa ta amince ya ciyo sabon bashin naira tiriliyan 1.7 domin cike gibin kasafin kudin 2024


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya rubutawa majalisar dokokin kasar wasika domin ta amince ya sake cin sabon bashin Naira Tiriliyan 1.7 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2024.


Kakakin majalisar dokoki Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar da shugaba Tinubu ya aikawa majalisar, a yayin zaman majalisar na ranar Talata.


Wannan na zuwa ne bayan da a 'yan kwanakinnan babban bankin Najeriya CBN ya ce gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 domin biyan basussukan kasashen waje da ake bin kasar cikin watanni tara na farkon shekarar 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp