Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rushe majalisar gudanarwa ta jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke jihar Anambra

Shugaba Tinubu

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar ya ce rushe majalisar gudanarwar ya biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa akwai wasu abubuwa da majalisar ke yi ba bisa ka'ida ba.


Gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda majalisar ta nuna rashin kula da dokokin jami’ar wajen zaben wasu shugabanni.


Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya kuma rushe shugabancin Engr. Ohieku Muhammed Salami a matsayin Pro-chancellor kuma shugaban majalisar gudanarwa na jami'ar tarayya ta kimiyar lafiya dake Otukpo a jihar Benue.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp