Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Assimi Goïta ya nada Janar Abdoulaye Maïga a matsayin sabon firaministan kasar
Kwana daya da tsige Choguel Kokalla Maïga biyo bayan wadansu kalamai da ya yi a kan shugabannin sojojin, inda ya zarge su da kin son maida mulki ga farar hula.