Shugaba Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa 7 a ranar Litinin

 



Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa guda 7 da ya nada a makon jiya


Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban na Nijeriya ya fitar a ranar Lahadi 



Ministocin da za a rantsar sun hada da;


1. Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu wacce aka naɗa ta ministar ƙasa a ma'aikatar harkokin waje.

 

2. Jumoke Oduwole matsayin ministar masana’antu da kasuwanci da zuba jari.


3. Dr Nentawe Yilwatda ministar jin ƙai.


4. Muhammadu Maigari Dingyadi matsayin ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi.


5. Idi Mukhtar Maiha ministan ma’aikatar kiwo.


6. Yusuf Abdullahi Ata matsayin ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane.


7. Dr Suwaiba Sa'id Ahmad da ta zama sabuwar ministar ilimi.


A ranar 23 ga watan Oktoba ne dai shugaban na Nijeriya ya sanar da korar ministoci 5 daga gwamnatinsa bisa laakari da rashin kwazon su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp