Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja a gobe Laraba domin karba gayyatar shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga, ya ce ziyarar shugaban ta kwanaki uku zata mayarda hankali wajen karfafa alakar shugabanci, tattalin arziki da al'adu da kuma hadaka tsakanin kasashen musamman a dannin noma, tsaro, ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa da dai sauransu.
Shugaba Tinubu zai samu rakiyar uwar gidansa da kuma wasu jami'an gwamnati.
Category
Labarai