Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai gabatarwa zauren majalisar dokokin kasar kudirin kasafin kudi na shekara ta 2025 a gobe Laraba.
Sakataren yada labarai na majalisar Dr Ali Barde Umoru wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan, ya bukaci jerin sunayen 'yan jarida da zasu halarci zaman.
A makon da ya gabata majalisar tattalin arziki ta kasar ta amince da naira tiriliyan 47.9 a matsayin kasafin kudin 2025.
Category
Labarai