Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisa, yana neman ta amince da nadin Janar Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasa na Nijeriya




A cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Hon Tajuddeen Abbas, Shugaba Tinubu ya bukaci majalisun sun tabbatar da nadin bisa la'akari da tanadin doka a sashe na 218(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka yi wa gyara a 1999 da kuma sashe na 18(1) na dokar da ta kafa rundunar soji.


Shugaba Tinubu dai ya nada Janar Oluyede a matsayin mukaddashin babban hafsan sojin kasa na Nijeriya a ranar 30 ga watan Oktoba, 2024 bayan jinya da Janar Lagbaja ya tafi, ba a ma jima ba, Janar Lagbaja ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba.

Kafin nadin nasa, Janar Oluyede shi ne kwamandan rundunar sojin kundumbala da ke Jani, jihar Kaduna.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp