Tinubu ya yi wannan karramawar ne a yayin jana'izar babban hafsan sojin kasa na Nijeriya da aka gudanar a Abuja.
Jana'izar ta samu halartar shugabannin majalisa da na tsaro da manyan jami'an gwamnati.
Shugaba Tinubu ya ce sadaukarwar marigayi Taoreed Lagaja ba zata tafi a banza ba.
Tuni dai aka binne gawar babban hafsan sojin kasa na Nijeriya marigayi Janar Taoreed Lagbaja.