Tinubu ya karrama Firayim Minista India da lambar yabo ta GCON
Shugabam Nijeriya Bola Tinubu ya bai wa firaministan kasar Indiya, Narendra Modi babbar lambar yabo ta GCON
Shugaban kasar ya karrama firaminista Modi a wani taro da ke gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Lambar girmamawa ta GCON ita ce ta biyu mafi girma a Nijeriya, bayan ta GCFR da aka kebe shugabannin kasar
A ranar Asabar ne dai Narendra Modi ya iso Nijeriya domin wata ziyarar aiki da zai gabatar kan yadda za a kara kulla kyakkawar dangantaka tsakanin kasashen biyu