Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta samu tallafin dala miliyan $2.5m daga hukumar ba da agaji ta kasar Saudiyya domin a tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke fuskantar kalubalen jin kai.
Kwamishinan ayyukan Agaji na jihar Musa Kainuwa ne ya bayyana haka a taron horar da likitoci na kwanaki biyar da aka kammala ranar Juma’a.
Jihar Zamfara na daga cikin jerin jihohin da ke dama da matsalar tsaro da ta yi sanadiyar raba iyalai da dama da gidajensu