Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya musanta ikirarin cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohi a Nijeriya, yana mai cewa sarakunan gargajiya ne ke mulkin kasar tun kafin yanzu, inda ya ce a matsayinsu na sarakuna sun fi gwamnoni fahimtar kasar.
Sarkin Musulin ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan ci -aban matasan Arewacin Najeriya da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ta shirya a Abuja ranar Talata.
Alhaji Sa'ad Abubakar ya ce sarakuna na mutunta kawunansu ne ta hanyar kauce wa tsoma baki kan al'amurra, yana shugabannin na gargajiya na mutunta ikon da gwamnoni ke da shi a jihohin. Ya ce bai kamata a dauki hakan a matsayin tsoro ba.