Ra'ayin Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu da kuma Sanata Shehu Sani sun yi hannun riga game da kudurin gyaran dokar haraji ta kasa da ke gaban majalisar dokoki ta kasa.
Sanata Ndume a cikin wani bayani da ya fitar a Abuja, ya ce dokar ba ta da hurumi a wannan lokacin, musamman lura da halin matsin rayuwa da al'ummar Nijeriya ke ciki.
Sai dai tsohon Sanata Shehu Sani na ganin cewa wannan dokar zata amfanar da 'yan Nijeriya, kuma jihohi zasu karbi harajin kayayyaki daga kamfanoni a maimakon su turawa gwamnatin tarayya.