Samar da ayyukan yi, ba aikina ba ne - Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi


Ministan Kwadago da ayyukan yi Maigari Dingyadi, ya ce sun yi wa ma'aikatarsa gurguwar fahimta domin samar da ayyukan yi bai cikin aikinsa.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron shekara shekara na cibiyar jami'an hulda da jama'a ta kasa wanda ya gudana a Abuja.

Duk da cewa ma'aikatar na sane da ƙaruwar matasa da basu aikin komi, Maigari Dingyadi ya ce samar musu da ayyukan yi, ba ya daga cikin manufofin ma'aikatar sai dai ta samar da yanayin da za su yi aikin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp