Mai ba shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama’a, Sunday Dare, ya yi kira ga yan kasar sa su yi hakuri kan korafe-korafen da ake ta yi na garambawul din da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi.
Ya ce shugaban kasar yana aiki tukuru domin yadda ‘yan Najeriya za su ci gajiyar sake fasalin gyaran tattalin arziki da gwamnati ke yi a halin yanzu
Dare ya ce shugaban ya cancanci a yaba masa kan wadannan manufofin duk da cewa suna sa tsauri amma za a ga amfanin su nan gaba