Rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutum 82 cikin mako biyu


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gabatar da mutum 82 da ta cafke bisa zargin da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar. 

Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce daga cikin wadanda suka kama akwai mutum 13 da ake zargi da fashi da makami, da mutum 13 da ake zargi da sata, da wasu yan daba 35. 

Akwai mutum 12 da ake zargin dilolin ƙwaya ne, sai m mutum 5 da ake zargi da aikata zamba da mutum da ake zargi da satar mashin da kuma garkuwa da mutane. 

Kakakin rundunar ya ce su kwato bindiga kirar AK47 da bindiga 3 samfurin gida da wayoyin hannu 10 da kuma wasu miyagun makamai.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp