'Yan sanda |
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Dalijan ne ya bayyana haka a Gusau ranar Talata.
Ya ce ‘yan sandan sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda 16, a atisaye daban-daban a cikin makonni uku da suka gabata.
Ya kara da cewa sun kuma samu nasarar kwato bindiga kirar Pistol da aka kera a cikin gida daga hannun wani da ake zargi da ke kera makamai da ke Jos, Filato.
A cewar sa bisa bayanan sirri da suka samu sun gano tare da kama wani mai kera makamai a Jos, kuma sun bi sawun wani da ake zargi da safarar makamai daga Aljeriya a kan iyakar Illela inda suka samu nasarar kama shi.
Wanda ake zargin dan kasar Algeria, ya shaidawa ‘yan sanda cewa ya shafe shekaru takwas yana aikata wannan laifin.